4 Mayu 2020 - 03:41
Jami’an Tsaron Masar Sun Halaka ‘Yan Ta’adda 18 A Yankin Sinaa

Ma’aikatar tsaron kasar Masar ta bayar da sanarwar cewa sojojin kasar sun kashe akalla yan ta’adda 18 a garin Bir-Abd dake yanki Sina a wata fafatawa da suka yi da su a maboyarsu.

(ABNA24.com) Ma’aikatar tsaron kasar Masar ta bayar da sanarwar cewa sojojin kasar sun kashe akalla yan ta’adda 18 a garin Bir-Abd dake yanki Sina a wata fafatawa da suka yi da su a maboyarsu.

Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin kasar tana cewa sun sami an tsegunta masu inda ‘yan ta’addar suke a garin na Bir-Abd kafin su farwa jami’an tsaron kasar.

A musayar wutar da suka yi a nan take sun kashe ‘yan ta’adda 18 sannan sun gano tarin makamai a maboyar tasu, wadanda suka hada da bindigogi, kayayyakin yaki, da kuma damarar bama- bamai da sauransu.

Labarin ya kara da cewa ‘yan ta’addar suna shirin kai hare- hare kan jami’an tsaron kasar ne a wurare daban –daban a duk fadin yankin na Sinaa.

Kafin wannan sanarwar dai shugaban kasar ta Masar Abdulfattah Assisi ya bayyana a cikin shafinsa na twitter cewa wasu yan ta’adda sun kashe jami’an tsaron kasar a garin Bir-Abd.


/129